Kwace sansanin Chenaya a gundumar Gomarcha dake lardin Faryab da aka yi a daren jiya litinin na zuwa ne bayan kwanaki biyu da aka kwashe ana gwabza kazamin fada.
Jami’ai sun ce mayakan sun sami nasarar kwace sansanin ne bayan da sojojin dake fafatawa da su suka kasa samun taimako ta kasa da ta sama, makamai da wasu kayayyakin su kuma suka kare.
Jami’an soji da na gwamnatin yankin sun tabbatarwa muryar Amurka yau Talata cewa, 40 daga cikin 70 na sojojin da aka girke a sansanin, sun mika wuya ga mayakan Taliban. Jami’an suka kuma ce ta yiwu an kashe sauran sojojin ko kuma sun tsere zuwa tsaunukan dake yankin a lokacin fadan.
Kwace sansanin Chenaya na zuwa ne bayan da jami’an tsaron Afghanistan, tare da taimakon hare-hare ta sama daga dakarun Amurka, da kuma shawarwari daga kwararru, suka taimaka wajen kwato birnin Ghazni mai muhimmanci a kudu maso gabashin yankin bayan wani kazamin fada da ‘yan Taliban.