Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Gada a Italiya ta Ruguje


Akalla mutane 11 sun mutu a yayinda bangaren wata gada da motoci kusan 10 ke kanta, ya ruguje yau Talata a lokacin wani ruwan sama kamar da bakin kwarya a arewacin birnin (jenowa) Genoa, kamfanin dillancin labaran kasar Italiya ne ya bayyana haka, inda ya ambaci ma’aikatar cikin gidan kasar.

Ministan sufurin kasar, Danilo Toninelli ya ce yana bibiyar lamarin da za a kira mummunan bala’I cikin fargaba.

Wani ganau ya fadawa gidan talabijin din Sky Italia cewa ya ga motoci 8 zuwa 9 akan gadar a lokacin da ta ruguje, abinda ya ce tamkar tashin duniya ne.

Kamfanin dillancin labaran ANSA ya bayyana cewa hukumomi na ganin rashin ingancin gadar da aka gina a shekarar 1960 kuma aka yi mata gyare-gyare a shekarar 2016 ne ya janyo rugujewar ta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG