Wasu Sassan Kasar Nijar Na Fama Da Karancin Abinci

Najeriya 'yan gudun hijira a Nijar, Mayu 6, 2015.

Kamar arewa maso gabashin Najeriya, wadansu sassan Nijar na fama da karancin abinci sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram. Duk da yake ba a ayyana yunwa ba, karancin abinci da kuma rashin abinci mai gina jiki wata matsala ce da ake fuskanta zahiri.

An girke daruruwan ‘yan gudun hijira daga Najeriya da kuma wadanda hare haren kungiyar Boko Haram suka raba da matsugunansu a Jamhuriyar Nijar, a wani sansanin Assaga dake tazarar kilomita kalilan da Diffa, wadanda kuma suke rayuwa hannu baka hannu kwarya kowacce rana. Ana ganin kananan yara dake fama da rashin abinci mai gina jiki a sansanin.

Bisa ga cewar asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF, kimanin kananan yara kasa da shekaru biyar dubu goma sha biyu suke fama da cutar rashin abinci mai gina jiki a Diffa.

Bisa ga rahoton shirin samar da abinci na duniya, kimanin mutane miliyan daya da dubu dari biyar ne a jamhuriyar Nijar suke fuskantar barazanar karancin abinci, wadanda basu da takamammiyar hanyar samun abinci mai gina jiki.