Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Nijar da Taimakon Ofishin Jakadancin Amurka Sun Bude Kasuwar Baja Koli


Kasuwar Baja Koli
Kasuwar Baja Koli

A kokarin karfafa wa matan Nijar kwarin gwuiwar bude nasu masana'antu ya sa kungiyar matan Nijar ta shugabannin kasuwanci tare da goyon bayan ofishin jakadancin Amurke bude kasuwar baje koli inda mata suka nuna irin kayan gargajiyan da suka kirkiro

Madam Hauwa Idi ta cibiyar wata kungiyar kasuwanci na cikin wadanda suka shirya bude kasuwar da ta hada da matan sassan Nijar.

A cewarta sun zo ne su gwada kwarewar mata bisa abubuwan da suka iya yi. Zasu duba su ga menene kowace mace ta iya yi cikin rayuwarta domin samun dogaro ga kai. Menene ta koya cikin rayuwarta da zai taimaka mata da 'ya'yanta da iyalanta.

Wadanda suka baje hajjojinsu a kasuwar ta cibiyar raya al'adun Amurka sun yi yaba da damar da aka basu. Wata Baraka Musa tace basu damar baje kolin alheri ne garesu. Tana mai cewa a irin wannan kasuwar kamata yayi su mata su sanya kayansu na gargajiya zuwa cikinta domin su nunawa duniya suna son kasarsu..

Wata Hajiya Halima ta kawo kaya iri-iri da ta sarrafa daga Agadez.

An kebe wani lokaci na musamman domin manyan mata 'yan kasuwa su fadakar da kawunan 'yan mata sirin soma na sana'o'in tare da kafa masana'antunsu.

Adama Abubakar wata daliba da ta halarci kasuwar nada burin kafa nata kamfanin idan ta kammala karatu. Tace tana da burin kafa makarantar da zata dinga koyas da 'yan mata sana'o'in hannu koda ma suna zuwa makaranta. Tace tana son tayi hakan ne saboda 'yan mata su samu suyi aik duk da cewa 'yan matan sun fi son yin aure.

Kasuwar Baja Kolin kayan da matan Nijar suka kirkiro
Kasuwar Baja Kolin kayan da matan Nijar suka kirkiro

Ministan bunkasa ayyukan hannu da yawon bude ido Ahmed Moto ya yaba da tallafin da kasar Amurka ke ba kasar ta Nijar da nufin inganta rayuwar al'umma. Yace baje kolin ya kara jaddada hakan.

Kasuwar Baja Kolin da matan Nijar suka kirkiro
Kasuwar Baja Kolin da matan Nijar suka kirkiro

Jakadiyar Amurka tace kasarta ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen taimakawa Nijar musamman mata domin su inganta rayuwarsu tare da habaka tattalin arzikin kasar. Ko yanzu ma Nijar na cin gajiyar taimaon kudi daga Amurka da suka dara dala miliyan dari hudu na inganta rayuwa a karkara.

Ga rahoton Sule Mummuni Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG