Wasu fitattun sanatoci ‘yan jam’iyar Republican su uku, sun ce ba za su kada kuri’ar da za ta soke wani bangaren dokar da ta samar da tsarin kiwon lafiyar kasar ba, har sai sun samu tabbaci daga shugabannin majalisar cewa, ba za su amince da tsarin ba “kamar yadda yake” a maimakon haka, sai sun amince a tattauna kan wani ingantaccen tsari da zai maye gurbin shirin kiwon lafiya na Obamacare.
A farkon makon nan, sau biyu ‘yan Republican da ke majalisar dattawa suka gaza soke tsarin kiwon lafiyar na Obamacare, wanda da aka kwashe shekaru bakwai ana amfani da shi, a yunkurinsu na: ko su soke dokar da ta samar da tsarin baki daya, ko kuma su soke shi su maye gurbin dokar da wata daban.
A jiya Ahamis, jam’iyar Republican, ta yi yunkurin neman kuri’un da za su ba da damar amincewa da abinda ‘yan Republican din suka kira da “kudiri mara auki” da zai kawar da shirin kiwon lafiyar mai rahusa na Obamacare, wanda hakan na nufin, za a kawar da sharadin tsarin kiwon lafiya na Obamacare da yake tilastawa Amurka su yi amfani da shi ko kuma su biya tara, wanda har ila yake tilastawa ma’aikatu su baiwa ma’aikatansu kariyar ishorar lafiya.