Kungiyar Arewa Citizen Action for Change ta ce 'yan majalisar dokokin Najeriya su yi tunani
WASHINGTON,DC —
Kungiyar Arewa Citizen Action for Change ta wasu matasan arewacin Najeriya ta yi ishara ga 'yan majalisar dokokin Najeriya game da bukatar da shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar ta neman izinin tsawaita dokar ta baci a jahohin Borno da Yobe da Adamawa wadanda ruwan rikici ya ciwo a yankin arewa maso gabashin kasar Najeriya.
Wanda yayi magana da yawun matasan, Mallam Ashir Sharif ya ce babu tasirin da karin dokar ta bacin zai yi a wadannan jahohi guda uku, saboda an gani a baya, ba a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.
Wakilin Sashen Hausa a Kaduna Isah Lawal Ikara ne ya hada rahoto:
Your browser doesn’t support HTML5