Wasu Matasa Sun Bijirewa Bangar Siyasa a Kogi Da Pilato

Wasu Matasa a Najeriya

Wasu Matasa a Najeriya

Wasu matasa daga jihohin Pilato da Kogi sun bayyana kudirinsu na bijirewa shiga bangar siyasa da haddasa fitina a kasa.

Matasan su 98 da hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka suka sami horo na musamman a cibiyar koyar da dabarun shugabanci da zama dan kasa na gari, dake Shere Hills a jahar Pilato, sun bayyana cewa yanzu dai kansu ya waye don ba zasu yadda a kara amfani dasu wajen haddasa tashin hankali ba.

Darakta janar na cibiyar koyar da dabarun shugabanci da zama dan kasa na gari, Jonah Bawa, ya ce cikin makonni biyu da matasan suka yi a cibiyar, sun sami canjin rayuwa.

Jami’in hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, Segun Olusola, ya ce hukumar za ta ci gaba da taimaka wa matasa su cimma burinsu na rayuwa.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Matasa Sun Bijirewa Bangar Siyasa a Kogi Da Pilato - 3'43"