Daruruwan matasa ne su ka yi tattaki daga farfajiyar da ake kira "Place Wifi' dake birnin Yamai zuwa 'rond point des marthyrs' dake gab da gabar kogin Isa, wato fleuve Niger inda suka gudanar da wani gangami da nufin jan hankulin shugabannin duniya akan bukatar mutunta alkawulan da suka dauka game da batun yaki da illolin canjin yanayi.
Issa Garba, daya daga cikin shugabannin kungiyar JVE, shine kan gaba a wannan yunkuri.
A Jamhuriyar Nijer, kamar sauran kasashen yankin Sahel, na daga cikin kasashen dake dandana kudarsu sanadiyar dumamar yanayi. Dalili kenan da matasan kasar suka tashi tsaye don ankarar da mahukunta akan wannan matsala, in ji Nafissa Hassan Alfari, wata ‘yar gwagwarmayar kare muhalli.
Jinkirta zartar da matakan dakatar da abubuwan dake haddasa dumamar yanayi, wani abu ne da aka hango cewa yana barazana ga dorewar rayuwar halittu, nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa.
Your browser doesn’t support HTML5