Matan sansanin suna korafin cewa ba'a basu abinci isasshe lamarin da suka dauka kamar an manta dasu ne.
To saidai shugaban hukumar samar da agajin gaggawa na jihar Ahmed Satome yace zargin da matan keyi ba gaskiya ba ne. Ya amince an samu jinkiri watan jiya saboda kuskure amma yanzu an daidaita lamuran
Wannan tada hammatan da suka yi ya auku ne lokacin da kwamitin sulhu a karkashin shugabancin Ambassador Matthew Rycroft da wasu jakadu 13 ke ziyarar sansanonin 'yan gudun hijira dake jihar Borno da sauran wurare a arewa maso gabas.
Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta isa Teachers' Village yayinda yamutsin ya gudana.
Matan da suka yi magana sun ce suna neman shekaru ukku ke nan cikin sansanin ba tare da sanin ranar da zasu koma garuruwansu ba. Sun ce abinci baya isansu. Sun ce awon mudu biyu ake basu kowane wata ko su nawa ne cikin iyali daya. Misali mai mace daya da yara biyar mudu biyu kawai za'a bashi su ci wata guda.
Matasa maza da mata suna zina,'yan matan na daukan ciki suna zubarwa kana matan musulmi fita suke yin bara yayin da wasu coci suna taimakawa matan kiristoci. Bugu da kari yara basa makaranta.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5