Wasu Masoya Kungiyar Kwallon Kafar Barcelona 12 Sun Gamu Da Ajalinsu

Kimanin mutane 12 masoya kungiyar kwallon kafar Barcelona SC suka mutu, kana mutane 30 suka raunana, a wani hatsari da ya same su lokacin da suke dawowa daga kallon wasanni, daga garin Cuenca.

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyanar da abun da ya haddasa hatsarin ba, kungiyar ta Barcelona na daya daga cikin kungiyoyin dake da mafi rinjayen masoya a kasar. A cewar shugaban kungiyar masoya kungiyar Jose Cevallos, ya bayyana cewar labarin yazo masu cike da mamaki.

Sai ya kara da cewar za a shirya jana’izarsu a babban filin kwallon kasar don karrama magoya bayan kungiyar kwallon kafa a kasar ta Ecuador sun bayyana alhinin su da yi ma mamatan fatan alkhairi.

Hadarin ya faru ne akan hanyar Cuenca, kusa da garin Molleturo da misallin karfe 10:00pm. Jami’an kamfanin sufurin kasar ta Ecuador sun bayyana cewar za a gudanar da bincike don gano dalilin afkuwar hatsarin, mun sami wannan labarinne daga shafi google.