Wannan hatsari dai ya faru ne a kusa da garin Mbanga, wanda da ke da tazarar kilomita 80 daga birnin cinikayyar Douala, an dai samu asarar rayukan mutane 17, haka kuma wasu da dama sun jikkata inda aka garzaya da su babban Asibitin garin Mbanga.
Cikin kowanne makwanni biyu zuwa uku ana samun asarar rayukan mutane sama da 60 domin rashin kyawun yanayin hanyoyi a Kamaru.
Wakilin Muryar Amurka Garba Awal, ya zanta da daya daga cikin mutanen wannan hatsari ya rutsa da su. Wanda yace sunyi tayiwa Direbansu magana kan cewa yana gudu dayawa amma yayi biris da su, sai gashi yanzu ana maganar mutane sun rasa rayukansu.
Shima Mallam Sa’ad, wani mai zirga zirga kan hanyoyin kasar Kamaru yace tabbas hanyoyin basu da kyau ga kuma kankanta, ya kumayi tsokaci kan yadda gwamnatin kasar ta saka ido ba tare da yunkurin magance wannan matsala ba.
Wannan lamari dai ya zama ruwan dare akan hanyoyin kasar Kamaru, kasancewar rashin kula da kuma shakulatin bangaro da hukumomi keyi a kasar.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5