Manoman Shinkafa Sun Koka Akan Bada Lamunin Noma Na Najeriya

Wasu Manoman Shinkafa a Najeriya

Manoman shinkafa a jihohin Kano, Jigawa da Katsina sun koka game da tsarin bada lamunin kayan noma karkashin shirin gwamnatin tarayya na tallafawa masu noman karkashin kulawar babban bankin kasar.

Tun a shekarar 2016 ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin bada lamanin kayan noman da nufin bunkasa noman shinkafa a karkashin tsarin ta na dakile shigo da shinkafa cikin Najeriya daga ketare.

Alhaji Yakubu Tagahu, wani manomin shinkafa daga yankin karamar hukumar Takai a jihar Kano ya yi korafi akan rashin isassun kayan aikin noman shinkafa da suke fama da shi.

Shi kuwa Malam Husssaini Dutse daga jihar Jigawa cewa yake, kayayyakin da aka basu a matsayin bashi karkashin wannan shirin sun fi tsada idan kwatanta da wadanda ake sayarwa a kasuwa.

Shi kuma Alhaji Rabe Yusuf daga jihar Katsina, daya daga cikin manoman da suka karbi bashin karkashin wannan tsarin na bada lamanin noman shinkafa ya fadi cewa sun karbi bashin kayayyaki amma basu san farashen su ba, kuma akan basu kayayyakin a kurarren lokaci.

Kungiyar manoman shinkafa da ake kira RIFAN a takaice, ita ce babban bankin kasa na CBN ya dorawa nauyin raba kayayyakin ga manoman. Kungiyar manoman shinkafar a cewar sakatarenta, Alhaji Ado Hassan Yakasai da yake maida murtani akan korafin manoman, yace babu abinda aka karawa kudin da ya wuce kima.

Ga karin bayani cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Manoman Shinkafa Sun Koka Akan Rashin Kayan Aiki - 3'32"