Wasu manoman rani sun zargi gwamnatin gwamnatin Borno da datse masu ruwa sakamakon ginin wasu gadoji a cikin birnin Maiduguri da gwamnatin ta yi.
Yanayin rashin samun isasshen ruwa da zai taimakawa aikin lambun da suke yi, ya jefasu cikin wani mawuyacin hali, saboda gonakain nasu sun soma bushewa.
Alhaji Muhammad Shuwa, shugaban manoman, yace sun rasa madafa, domin sun dogara da aikin lambu ne kacokan. Yace sun yi iyakacin kokarinsu, amma ba'a bude masu ruwa ba. Yace gina gadoji da suke yi sun toshe ruwa, shi ya sa basa samun ruwan noma.
Amma gwamnatin jihar Bornon, tace batun ba gaskiya ba ne. Tace ita bata datse masu ruwa ba, a cewar kwamishanan aikin gona na jihar, Alhaji Muhammad Gili. Yace karin yawan masu anfani da ruwan ya jawo masu matsala. Da akwai manoma goma yanzu sun fi talatin da suke anfani da ruwan. Kowa idan ya bude ruwan, wadanda suke nesa ba zasu samu isasshen ruwa ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5