Wasu Kananan Jam'iyyun Siyasa Sun Hade Da manyan Jam'iyyu Gabanin Zaben Gwamnoni

Masu iya magana na cewa "idan aski ya zo gaban goshi yafi zafi." Ga dukkan alamu haka zancen yake idan aka yi dubi da halin da kananan jam’iyyu suka sami kansu a ciki, wanda ala tilas ya sa su yin mubaya'a ga manyan jam’iyyun kasar.

A jihar Bauchi ga missali, jigo a siyasar Najeriya Alhaji Bello shine ya jagoranci kananan jam’iyyun siyasa guda 33 da kuma 'yan takarar gwamna su 20, don ayyana goyon bayan su ga tsohon ministan tarayya Alhaji Bala Muhammed Kauran Bauchi na Jam’iyyar PDP.

A makwabciyar jihar Bauchi, wato jihar Gombe, shugaban hadakar jam’iyyun jihar Alhaji Muhammadu Garba,shine ya jagoranci kananan jam’iyyu guda 44 da 'yan takarar gwamna guda 14 don bayyana goyon bayansu ga Alhaji Inuwa Yahaya na jam’iyyar APC.

To sai dai kuma jigo a siyasar Najeriya Injiniya Sa’ad Abubakar Abullahi, Majidadin Gombe, yace gazawar kananan jam’iyyun ta fusakar kudaden tafiyar da jam’iyun ya zamo dole su nemi iyayen gida saboda suna sa ran in an kafa gwamnati zasu sami wani abu.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Kananan Jam'iyyun Siyasa Sun Hade Da manyan Jam'iyyu Gabanin Zaben Gwamnoni