Wasu Jiga-jigan Democrat Na Fuskantar Yiwuwar Rasa Kujerunsu

Wasu jiga-jigan jam’iyyar Democrats da dama na fuskantar yiwuwar rasa kujerunsu a majalisar dokokin tarayyar Amurka, bayan da aka kada kuri’a a zabukan fidda dan takara, da aka gudanar a jihohi hudu ranar Talata.

Wani tsohon shugaban kamaramar makarantar firamare mai suna Jamaal Bowman, wanda bai ma taba tsayawa takara ba, ya sha gaban dan majalisa kuma shugaban Kwamitin Harkokin Waje, Eliot Engel da kashi 61% na kuri’un akasin 36% a zaben da aka yi na keke da keke.

To sai dai jami’an zabe a birnin New York sun ce ayi hattara, saboda ganin cewa akwai wasu kuri’un da aka kada ta akwatin gidan waya, wadanda ba za a iya kirga su ba sai zuwa makon gobe, don haka sanin sakamakon zaben da aka gudanar ranar Talata zai dan dau lokaci.

To sai dai Bowman ya bayyana kwarin gwiwar yiwuwar yin nasara a karshe, yayin magana da magoya bayansa da yammacin ranar Talatar, ya na mai cewa, “Ina dokin zuwa majalisa don in tayar da hankali ga mutanen da ke wurin, wadanda su ka yi ta kare tsarin da ke hallaka ‘ya’yanmu.”