Rahotanni daga Afghanistan sun ce wasu munanan hare-hare da aka kai da wata mota dauke da bam da kuma hare-haren bindiga a Kabul babban birnin kasar, sun yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.
Jami’ai sun ce an kwashe sa’o’i shida ana arangama tsakanin masu gwagwarmaya da jami’an tsaron kasar bayan wata kawanyar da aka yi.
Kungiyar Taliban ta dauki alhakin shirya kai harin kunar bakin waken akan wurin da ta ce cibiya ce da ake tsare-tsare na tsaron kasar ta Afghanistan.
Mazauna birnin sun ce fashewar bom din ta yau Litinin ta faru ne a tsakiyar birnin da safe lokacin da ake gaggawar zuwa aiki, abin da ya sa hayaki ya turnuke sararin samaniyar birnin Kabul.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar, Nasrat Rahimi, ya fada a wata sanarwa cewa, ‘yan bindiga da dama sun labe a kusa da wani dogon bene da ake ginawa bayan fashewar bom din kuma suka yi ta bude wuta akan ‘yan sanda Afghanistan da suke kan aiki a lokacin.