Batun kalubalen musayar kudaden ketare da karbar haraji barkatar daga hannun direbobin motocin dakon kaya dake jigilar kayayyakin masarufi da wadanda masana’antu ke sarrafawa zuwa sassan Najeriya, na daga cikin al’amuran da kwamitin ya gano cewa suna taka rawa wajen hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa da ‘yan kasar ke fuskanta.
Haka kuma kwamitin ya lura da cewa tsadar man gas da motocin dakon kaya ke amfani da shi, da kuma kudaden na goro da jami’an tsaro kan karba a hannun direbobin na ‘kara dagula lissafin farashin kayayyaki a Najeriya.
Shugaban shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya na kungiyar mamallaka motocin tanki da na dakon kaya, Alhaji Sani Sambo Dan Fulani, yace ya kamata gwamnati ta duba wanne tallafi direbobin ke bukata musamman ma na bangaren kayayyakin mota da ake shigowa da su daga kasashen waje, da kuma samar da man gas da suke amfani da shi, hakan zai tallafa wajen rage tsadar dakon kaya.
Kasancewa abubuwan da suke haifar da tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya na da yawan gaske, amma akwai bukatar gwamnati ta dauki matakan gaggawa masu gajeran zango da nufin kashe kaifin wahalar da ‘yan ‘kasa ke ciki, inji Dakta Lawal Habib Yahaya, masanin kimiyyar tattalin arziki a jihar Kano.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.
Your browser doesn’t support HTML5