Wasu Gwamnonin APC Sun Damu da Rikicin Dake Kunno Kai a Jam'iyyarsu

APC

Wasu gwamnonin jam'iyyar adawa ta APC sun tabo wasu batutuwa da suka shafi dambarwar siyasar kasar da kuma zargin kasawar PDP da rarabuwan kawuna dake wakana a cikin jam'iyyarsu ta APC.

Gwamnonin na ganin rikicin dake kunno kai a jam'iyyar tasu ka iya hanata kwace mulki daga hannun jam'iyyar PDP a zaben 2015.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a fadar gwamnatin jihar Imo. Rochas Okorocha gwamnan jihar Imo yana da irin wannan tunanen. Yace idan da PDP tana aiki yadda yakamata da yau babu APC. Yace zuwa APC domin an gaji ne da yadda abubuwa suke tafiya. Amma damuwarsu yanzu a jam'iyyar APC shi ne hadin kan 'yan jam'iyyar. Idan basu hada kai ba ba zasu iya kwace mulki ba. Idan basu hada kai ba zasu sha wahala. Amma idan sun hada kai zasu kada PDP.

Shi ma gwamnan jihar Sokoto Aliyu Magatakardar Wamako kuma sarkin yamman Sokoto ya bayyana manufofin da zasu fito dasu yayin da Allah Ya basu ikon mulkin Najeriya. Jam'iyyarsu tana son taimakawa jama'ar Najeriya. Ta taimaka ta yi mulki tsakaninta da Allah ta tabbatar da adalci ga al'umma. Zasu kawo tsaro su samar ma mutanen Najeriya aiki. Gwamnatin yanzu ta kasa a wurare daban daban musamman wajen samar da tsaro. Ta kasa samar da ingantacen abinci da kiwon lafiya.

Barrister Ibrahim Jalo mataimakin kakakin jam'iyyar PDP yace a harakar Najeriya yau talakawa sun yi wayo sun gane ana wasa da hankanlisu. Yace Wamako da Okorocha suna cikin PDP ta habaka shi yasa yanzu har suna babatu da bakunansu da maganganun gangan. Lokacin da suke cikin PDP me yasa basu yi gyare gyaren da suke magana akai ba yanzu. Sabili da haa talakawa sunan suna jiran su zabi PDP.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Gwamnoni APC Sun Damu da Rikicin Dake Kunno Kai a Jam'iyyarsu - 3' 49"