Hedkwatar Rundunar tsaron Najeriya ta ce ta bankado shirin wasu “bata gari” na yin amfani da kakin sojoji a yayin zaben gwamnoni da za a yi
Asabar a jihohin Kogoi, Imo da Bayelsa don haddasa rudani.
Daraktan cibiyar samar da bayanai na hedkwatar tsaron, Manjo Janaral Edward Buba ya bayyana haka a wani taron manema labaru a Abuja.
Janaral Buba ya aike da sakon gargadi mai zafi ga duk masu son ta da rigima yayin zaben da su yi wa kansu kiyamullaili su canza tunani, in ba haka ba to za su yi mummunar nadama.
Da ya ke amsa tambayar ko ta yaya za a iya banbance sojojin Najeriya da na bogi kuwa, Janar Buba ya ce saboda matakai irin na tsaro ba zai yi dogon bayani ba, amma kuma za a yi wa ‘yan jaridun da ke a jihohin uku cikakken karin bayani
Daraktan cibiyar tattara bayanan ya yi karin bayanin cewa rundunar tsaron na daukar zaben da matukar muhimmancin gaske, don haka za a yi duk abin da ya dace wajen samar da tsaro yayin zaben.
Ya kara da cewa tuni ma an kai dakaru da kayan aiki don tunkarar duk wani kalubalen tsaro a jihohi ukun da za a yi wadannan zabubbukan gwamnoni.
Masanin kimiyyar siyasa Farfesa Abubakar Kari ya ce wannan gargadi na sojojin ya dace musamman ganin jihohi ukun da za a yi zaben wurare ne da dama can suna fama da kalubalen tsaro, musamman tashin hankali irin na siyasa.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5