Wasu Al'adun Gargajiya Na Neman Gushewa

Kamar yadda ko wace al’uma ke da al’adun gargajiya da ta gada tun kaka da kakanni, wadda jama’a ke gudanar da harkokin rayuwarsu bisa ga tsarin al’adar su, akwai alamun gushewar wasu da dama a sakamakon wasu dalilai kamar su addini, samun ci gaba na zamani, zamani da kansa da sauran wasu dalilai da dama.

Wasu daga cikin al’adun gargajiya na al’ummar Hausawa da suka gushe an manta dasu baki daya, suna da dama koda shike kowane zamani kan zo ne da irin nasa salon wanda a lokuta da dama kan shafi al’ada.

A shekarun da suka gabata, zamanin da ba a fara amfani da wayar sadarwa ta hannu ba, da alamun zumunci tsakanin al’umma gaba daya ya fi zama sahihi tsakanin jama’a. Matasa kan zanta da juna na loakci mai tsawo ba tare da wani abu ya dauke masu hankali ba.

Ku Duba Wannan Ma Da Gaske So Kan Hana Ganin Laifi?

Yara kanana kan ziyarci abokan wasansu a cikin makwabta, har ma su yi wasa tare, wasu lokuta ma har sukan ci abinci tare da juna, yanayin da ba kasafai ake samun sa a yanzu ba.

Ko kuna lura da wasu hanyoyin tafiyar da rayuwa a al’ummar ku ke nemen gushewa a hankali-a hankali?

Zaiayci shafin mu mai adireshi www.dandalinvoa.com domin a bayyana ra’ayi.