Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Gaske So Kan Hana Ganin Laifi?


Masu iya magana sun ce "so hana ganin laifi" lallai da alamun wannan batu haka yake domin kuwa, duk abin da ran dan adam ke kauna da wuya yake ganin aibun sa, koda sauran jama'a sun yi la'akari da shi.

Kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, shirin samartaka na dandalinvoa kan nemi jin ra'ayoyin matasa maza da mata akan batutuwan da suka shafi soyayya, zamantakewa da mu'amala da juna.

Tambayar da muka fitar a wannan karo ita ce "shin dagaske ne so na hana ganin laifi? ta yaya wannan zai kasance gaskiya a ce kawai dan kana kaunar abu sai idanunka su rufe har baka ganin laifin sa!.

Kadan daga cikin ra'ayoyin da muka samu sun sun tabbatar da wannan lamari sai dai wasu daga ciki sun bayyana cewa ba rashin ganin laifi bane, amma sun danganta shi da "kai zuciya nesa" a sakamakon nauyi ko kunya dakan shiga tsakanin masoya.

Me zaku ce game da wannan lamari kuma me nene ra'ayin ku akan wannan batu? shin da gaske ne so na hana ganin laifi?, ta yaya wannan ke shafar rayuwar jama'a baki daya?.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG