Wakilinmu sashen hausa na muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari ya tattauna da Alhaji Sule Lamido dangane da abubuwan da ya ambata a cikin wasikar dake bayyana burin sa na shugabantar Najeriya.
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya bayyana cewa idan jam’iyyar sa ta ga can-cantar ta tsayar da shi takarar shugaban kasa, ba yadda zai yi aiki shi kadai ba tare da hadin kan yan kasa gaba daya ba. Ya ce gina tittuna da inganta kasa mai saukin gaske ne amma zummunci da aminci shine mai wuya kuma sai an ci nasarar haka za a iya mulki.
Sule Lamido yace duk wanda yake shugancin Najeriya hakki biyu ne ya rataya a wuyan sa, na farko shine shugancin kasa, na biyu kuma shugabancin duk bakar fata na duniya.
Alhaji Sule Lamido ya kara da cewa su 'yan jammi’ar PDP sun san meyasa aka yi jamm’iar, kuma sun san amfanin kafa ta, haka kuma sun san inda suka yi kuskure, domin wasun su sun yi gangaci, wasu kuma sun azanci na dan’adam.
A cewar sa "idan mutum ya gano abin da yayi wanda ba dai dai bane sai mutum ya gyara". Tsohon gwamnan yace su kansu 'yan jam'iyyar PDP sun horu kuma suna da kisin Najeriya, a zukatan su. Yace baza su kara yin fushi don son zuchiyar mutum daya wanda zai yi sanadiyar ruguza kasa ba.
Ya kara jaddada cewa PDP na kishin Kasa Najeriya, kuma sun san ta karrama su, ta kuma mayar da su mututane, saboda haka suna da hakkin biyan adashin 'ya'yan Najeriya, na gobe.
Daga karshe Sule Lamido yace fatan sa shine idan aka tashi fidda wanda zai tsaya takarar shugabancin Najeriya, a fitar da wanda ya san hakkin Najeriya ya san amanar Najeriya, sannan kuma ya san hakkin ta a wajen duniya.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5