Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mata 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Tarwatsa Kawunan Su


Rahotanni daga jihar Borno sun bayyan cewa wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake sun tarwatsa kawunan su da misalin karfe takwas na daren asabar da kuma safiyar jiya lahadi a kauyen Dar dake karamar hukumar Madagali.

Yayin da yake hira da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Ibrahim Abdul’aziz, shugaban karamar hukumar Madagali, Hon, Muhammad Yusuf ya bayyana cewa maharan ‘yan mata ne kanana masu shekaru kasa da ashirin da biyar da haihuwa.

Shugaban ya kara da cewa ‘yar kunar bakin waken ta farko ta tayar da Bam din ne yayin da take ita kadai ba tare da ya raunata kowa ba, amma ta biyun ta raunata wata mata da ta tambaye ta yayin da take kokarin shiga jama’a, wadda a yanzu haka take karbar magani a asibiti.

Daga karshe Hon, Muhammad Yusuf ya bayyana cewa a koda yaushe karamar hukumar na cikin zaman dar-dar ne a sakamakon hare haren ‘ya’yan kungiyar boko haram, domin a cewar sa, jama’a da dama basa iya zuwa gonakinsu domin ko a satin da ya gabata an sace wasu mata guda uku, an sami guda biyu amma har yanzu babu duriyar ta ukun.

Daga Yola ga rahoton da Ibrahim Abdul’aziz ya aiko mana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG