Jaridar New York Times ta buga rahoto a jiya Litinin cewa Mutumin da ya shirya zaman tattaunawar da aka yi tsakanin Donald Trump Jr. (watau dan shugaba Donald Trump) da kuma wata Lauya ‘yar kasar Rasha a shekarar da ta gabata ya fada a wani sakon email cewa Gwamnatin Rasha ce ta bada bayanin da zai cutar da yunkurin Hillary Clinton na yin takarar shugabancin kasa.
Jaridar ta New York Times ta ce ta samo silar labarin ne daga wajen wasu mutane guda uku da ke da masaniya akan wasikar ta Email. Haka kuma sakon daga wani kusar fadakar da jama’a mai suna Rob Goldstone ya nuna cewa abubuwan da aka karbo na daga cikin yunkurin gwamnatin Rasha na taimakawa Donald Trump don ya kada Clinton a zaben.
Tattaunawar tsakanin Lauyar Yar Rasha Natalia Veselnitskaya a watan Yunin bara, wanda ya kasance haduwa ta farko tsakanin manyan jami’an kamfe na Trump da mukarraban Rasha a yayin Kamfe, yazo ne sati biyu bayan Trump yayi nasarar zama dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Republican, sati guda kuma kafin cibiyar tone-tonen silili ta wikileaks ta fara sakin sakonnin emails wadanda suka zama abin kunya ga Clinton.
Sai dai kuma lauyan Donald Trump Jr, Alan Futerfas ya karyata labarin da New York Times din ta buga, wanda yace babu wata gaskiya acikinsa”.