A watan Fabrairun da mu ke ciki ne ake sa ran za a fara tonon albarkatun man fetur da iskar gas da aka samu a Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Bauchi, Najeriya —
Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Bauchi ta kudu, Sanata Shehu Buba ne ya bayana hakan yayin da yake tattaunawa da gidan rediyon sashen Hausa na Muryar Amurka a Bauchi.
Yace Manajan Darektan kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ne ya shaidawa masa da Mai Bada Shawara Kan Sha’anin Tsaro na Kasa, Malam Nuhu Ribadu yayin da suka ziyarci ofishin kamfanin a Abuja.
A cewarsa, Manajan Daraktan ya ba da tabbacin cewa kamfanin da aka baiwa aikin hakar albarkatun man fetur din daga kasar Indiya ya iso Najeriya don fara
aiki gadan gadan a cikin wannan watan Fabrairu.
Ga cikakken rahoton Muhammad Abdulwahab:
Your browser doesn’t support HTML5