Wannan Ba Hurumin FIFA Bane

Gianni Infantino

Bayan fidda jerin sunayen ‘yan wasan kwallon kafa, mata da zasu gwabza wajan zaben, zakaran kwallon kafar Mata na duniya na shekara 2017, inda aka zabi ‘yar wasan tsakiya na kasar Amurka, Carli Lloyd, da ‘yar wasan gaba na kasar Holland, Lieke Martens, da Deyna Castellanos, mai shekaru 18, da haihuwa ‘yar kasar Venezuelan, wadanda zasu kara a tsakaninsu domin zamowa gwarzon 2017 a bangare kwallon Mata a duniya zaben yabar baya da kura.

Shaharariyan ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Amurka, mai suna Megan Anna Rapinoe, tace sam ba'a zabe wadanda suka dace ba,

Megan Anna, mai shekaru 33, da haihuwa ta bayyana cewa wadannan ‘yan wasa da aka bayyana sunayen su basu da kwarewa a fagen wasan kwallon kafa da zai basu cancantar a zabesu.

Tace yin haka yana nuna cewar hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA bata damu da sha'anin wasan kwallon kafar mata ba kenan domin tana nuna son kai wajan zaben ‘yan wasan da zasu yi takara a matakin gwarzaye.

Sai dai hukumar FIFA tace bata da hannu a cikin fidda sunayen ‘yan takarar domin ba huruminta bane,

FIFA tace kungiyar Masu horar da ‘yan wasa na kasashe da kuma kaftin kaftin na kungiyoyin kwallon kafa na kasashe daban daban da kuma kungiyar ma rubuta labarin wasannin kwallon kafa ne suke da hakki wajan zabin ‘yan takara.

Your browser doesn’t support HTML5

Wannan Ba Hurumin FIFA Bane - 5'39"