Tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya, irin su Kanu, Amokachi, Okocha, da Garba Lawal zasu halarci gasar farko na tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa da za a fara a jihar Bauchi, a watan Nuwamba 2017, wanda maigirma Gwamnan Jihar Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar zai kasance babban Bako.
An dai shirya gasar ne musamman domin tunawa da tsofaffin ‘yan wasa wadanda suka fafata a baya masu shekaru sama da arba'in da biyar 45, da haihuwa. Kuma ADC Gwamnan jihar Bauchi, DSP Adamu Ahmed, ne ya dauki nauyin gudanarwa.
A cikin wadanda zasu taka leda a wannan gasar akwai Pascal Patrick, wanda ya taba bugawa wa tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, da Baba Jibrin, wanda ya bugawa tawagar ‘yan kasa da shekaru 17, na Najeriya a Canada 1987.
Haka kuma tsofaffin kungiyoyin kwallon kafa 16, na Bauchi zasu kara a tsakaninsu a matakin rukuni rukuni, har a kai ga samu zakara.
DSP Adamu Ahmed ya ce ya saka wannan gasar ne domin bada gudumawarsa a matsayinsa na dan jihar kuma tsohon dan wasa da kuma tunawa da tsofin ‘yan wasan kwallon kafa da suka taka leda a baya da kuma karfafa dankon zumunci a tsakani al’uma.
Ya kuma yi alkawarin bayar da kyautar rigunan wasanni ga duk kungiyar da tayi rijista a gasar hade da kwallaye.
Facebook Forum