Wani sanannen lauyan dake kare hakkokin ‘yan luwadi ya babbaka kansa har lahira a birni New York na Amurka don nuna rashin jin dadinsa akan abinda ya kira muzanta muhalli.
Masu tafiya a kasa da kan babur sun ga konannar gawar David Buckel ranar Asabar din da ta gabata a wani filin hutawa dake Brooklyn. Kuma alamu sun nuna cewa kamar sai da Buckel ya jika kansa da man fetur kafin ya sanyawa kansa wuta.
Wata wasika da ya ajiye a gefen da ya kashe kansa ta ce “yana fata mutuwarsa zata ja hankalin jama’a akan bukatar kiyaye muhallin duniya.
“Yawancin mutane dake doron duniyar nan na shakar gurbatacciyar iska, dayawa kuma sun mutu da wuri sakamakon haka. Mutuwata na nuna sakamakon abinda muke yiwa kanmu,” abinda wasikar ta ce kenan a cewar jaridar New York Times.
Shekarun Buckel 60 da haihuwa yana kuma daya daga cikin sanannun manyan lauyoyin dake kare hakkokin ‘yan luwadi a Amurka. Ya sha kare masu auren jinsi da kuma yin tur da hana ‘yan luwadi shiga kungiyar Boys Scouts.
Daya daga cikin kararrakin da Buckel ya kere ita ce tsakanin Brandon da Richardson, inda aka gano cewa ofishin ‘yan sandan garin Nebraska yayi laifi wajen kasa kare rayuwar wani mutum da ya canza jinsin sa, da aka kashe.
Wannan shari’ar ce ta zama tushen wani fim da ya sami lambar yabo da ake kira “Boys Don’t Cry.