Yayin da ake fama da matsalar 'yan jagaliya na 'yan shila, yanzu haka wata matsalar da ke kara tada hankulan iyaye itace ta fyaden kananan yara, a lokacin da ake jimamin fyaden da aka yiwa wata karamar yarinya ‘yar shekaru biyar sai kuma ga wata sabuwa.
Inda jami’an rundunan tsaron farin kaya ta sibil defense suka samu nasarar cafke wani Malamin Firamare, Nathan Yusuf, da ake zargin ya yiwa wata daliba ‘yar shekaru 12 fyade da har ta samu juna biyu wato ciki.
Kwamandan rundunan tsaron farin kaya a jihar Adamawa, Abdullahi Nuruddeen, ya bayyana yadda lamarin ya faru da kuma matakin da za’a dauka.
Malam Suleiman Sanda Namtari, baffa yake ga wadda aka yiwa fyaden, ya bukaci abi kadun wannan lamari, domin zama darasi.
Yanzu haka dai tuni aka kai yarinyar da aka yiwa fyaden zuwa cibiyar kula da masu larurar fyade da ke asibitin kwararru na Yola, wato Hope Centre.
Shima wanda ake zargi da yiwa wannan yarinyar fyaden ya ce ya yi nadamar aikata wannan mummuna abu.
Yanzu dai an zura ido aga yadda shari’ar fyaden zata kaya.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:
Your browser doesn’t support HTML5