Ana sa ran cewa, wani babban masanin kimiyyar gwamnatin Amurka zai yi bayani a zaman majalisar wakilai a makon gobe, bayan ya kwarmata korafi yana zargin jami’ai da yin ramuwar gayya akansa a dalilin cewa, ya dage akan amfani da shawarwarin kimmiyya tare da ganin hukuma ta dage don yakar COVID-19.
‘Yar majalisar Anna Eshoo, ta ce korafin da Rich Bright yake yi alamu ne masu ta da hankali game da yadda gwamnatin Trump ke tunkarar annobar coronavirus, kana, ta ce zata bukaci sauraron bayanan sakataren lafiya da ayyuka Alex Azar da mataimakin sakataren shiri da kai dauki, robert adler.
Bayanan kwarmaton sunyi zargin cewa gwamnatin nan ta fi fifita abota (dangantaka) da rikicin tsakanin su fiye da kare lafiyar Amurkawa a wannan lokaci na annoba. Ta ce, korafin Dr. Bright na bukatar ayi masa nazari na tsanaki.
Bright ya ce, Kadlec ya matsawa sashin da yake jagoranta na binciken illimin hallitu, akan ya samar da rigakafi daga magungunan da basu da wani asali na kimiyya ciki har da maganin hydroxychloroquine.