Wani Kwamitin Majalisar Dattawan Amurka Ya Bada Umurnin Kiran Shaidu Akan Hunter Biden

Wani kwamitin Majalisar Dattawan Amurka a karkashin jagorancin 'yan jam’iyyar Republican ya bada umurnin kiran shaidu domin su bayyana abubuwan da suka sani a wani binciken da ake yi kan Hunter Biden, wato dan tsohon Mataimakin Shugaban kasar Amurka Joe Biden, wanda ya zama babban dan hamayyar Shugaban Amurka a zaben da za a gudanar a watan Nuwamba mai zuwa.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin tsaron cikin gida da kuma harkokin gwamnati, ya kada kuri’a kan batun kiran shaidun, inda aka kare da kuri’u 8 wadanda ‘yan Republican suka kada, yayin da ‘yan demokarats suka samu 6.

Zancen dai yana da alaka ne da wasu ayyuka da Hunter din yayi wa wani kwamfanin makamashi na kasar Ukraine mai suna Bursma.

Ciyaman din Kwamitin Sanata Ron Johnson ne ya bukaci da a gudanar da binciken, Johnson dai ya kara tado da binciken ne jim kadan bayan da aka gama shari’ar tsige Shugaban Amurka Donald trump.