Jami’ai a Afghanistan sunce wani harin kunar bakin wake na yau juma’a ya auna wani jerin gwanon motocin sojojin kasashen waje a Kabul, ya kuma hallaka akalla fararen hula 'yan Afghanistan 4 da kuma jikkata sojoji Amurkawa 4.
Sojojin Amurka sun tabbatar da kai wannan harin a babban birnin kasar Afghanistan, kuma sunce sojojin nasu sun samu “kananan raunuka” amma basu bada wani cikakken bayani ba.
Tuni dai kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin boma boman, wanda aka kai a wata babbar hanya da ake yawan zirga zirga da ta hada Kabul da garin Jalalabad da ke Gabashin kasar.
Sai dai kungiyar ta kara da cewa dan kunar bakin waken ya tada damarar boma boman ne a cikin motar da aka ajiye a kusa da gwammar jerin gwanon motocin sojojin kasashen waje.
Mai magana da yawun ministan harkokin cikin gidan Afghanistan, Nasrat Rahimi, ya ce mutane da dama da ke wucewa suna daga cikin wadanda suka samu raunuka.