Erdogan yana magana a ranar asabar, yace bayanan farko sun nuna cewa 'dan harin kunar bakin waken bai wuce tsakanin shekaru 12 zuwa 14 ba.
Yace ga bisa dukkan alamu kungiyar IS ce ta kai wannan harin a birnin Gaziantep, dake kusa da bakin iyakar Syria.
A cikin jawabin Erdogan na farko, yace kungiyar IS bata da banbanci da ta Kurdawan nan na PKK, da kuma mabiya Shehin malamin nan dake zaune nan Amurka Fetullah Gulen, wanda shugaba Erdogan yace yana da hannu dumu-dumu wajen yunkurin yi masa juyin mulki. A cikin watan da ya gabata.
A cikin sakon Erdogan yace abin da muke son mu fada wa masu kai mana hari shine ba za suyi nasara ba.
Fadar White House tayi Allah wadai da wannan harin da aka kai a birnin Gaziantep, tace masu wannan mummunar 'dabi'a su rasa inda zasu kai hari kuma sai wurin bikin aure.
A cikin sanarwar da aka fitar daga fadar ta White House tace mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, zai ziyarci kasar ta Turkiyya domin jaddada wa kasar aniyar Amurka ta aiki tare domin yaki da ta'addan ci.