Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bill Gate Zai Aika da Rigakafin Cutar Polio Najeriya


Bill Gates, hamshakin attajiri Ba'Amarike wanda ya bada gudummawar dala miliyan daya wa 'yan gudun hijira a arewa mmaso gabashin Najeriya yake kuma yaki da cutar Polio
Bill Gates, hamshakin attajiri Ba'Amarike wanda ya bada gudummawar dala miliyan daya wa 'yan gudun hijira a arewa mmaso gabashin Najeriya yake kuma yaki da cutar Polio

Bill Gates ya nuna damuwarsa akan sake bullar cutar shan inna a arewa maso gabashin Najeriya, kuma kamar yadda ya taimakawa 'yan gudun hijira ya yi alkawarin taimakawa har sai an ga bayan cutar

Mun yi matukar farin ciki da aka ce har an kwashe shekaru biyu ba tare da samun bullar cutar ba, amma kuma bamu ji dadi ba da aka ce an samu wasu yara biyu dauke da cutar a yankin tafkin Chadi a arewa maso gabashin Najeriya.

Yanzu mun dukufa ne wajen ganin cewa an aika da rigakafin cutar, ta yadda yara da dama za su samu, saboda ya zamanto babu wani yaro mai dauke da ita.

Ina da kwarin gwiwar cewa za mu iya, amma yanzu muna kokari muga yadda za mu tattara bayanai daga yankin kan bullar cutar saboda kada mu kuma samu aukuwar hakan a gaba.

Abin farin cikin shi ne, yakin da ake yi da cutar ta Polio har yanzu ana kai, a baya can Najeriya ce ke da kusan rabin yawan mutane da ke dauke da cutar a duniya, har mutane suna cewa ta ina zamu fara tunkarar matsalar.

Idan muka duba can yankin arewacin Najeirya, akwai matsaloli a fannin kiwon lafiya, amma idan muka samu muka kawar da cutar da ke bulla nan da can, to za mu shawo kan cutar baki daya.

Tsokacin Bill Gates Kan Sake Bullar Cutar Polio A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG