Wani Jirgin Horar Da Sojojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari Amma Matukan Jirgin Sun Tsira

jirgin da ya yi hatsari

Wani jirgi mai horas da sojojin saman Najeriya ya samu ‘yar karamar matsala a ranar Alhamis, amma matukan jirgin biyu da ke cikin jirgin sun tsira daga hatsarin, in ji rundunar sojin sama.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 1335 agogon GMT a kusa da filin saukar jiragen sama na sojoji a garin Kaduna da ke arewacin kasar a daidai lokacin da jirgin ke dawowa daga wani atisayen da ya saba yi, in ji kakakin rundunar sojin sama Edward Gabkwet a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce hukumomin sojin saman Najeriya sun ba da umarnin gudanar da bincike na farko don gano musabbabin hatsarin jirgin. Ba a bayar da ƙarin bayani ba.

Hadarin dai ya biyo bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu kirar MI-35P na sojin saman Najeriya da ya fada a cikin watan Disamba, kuma shi ne karo na uku da ya afku tun watan Yuli.