Sai dai shugaban kamfanin na Air France, Frederic Gagey, ya ce na’urar ba ta tattare da wata barazana.
Jirgin, kirar boing 777 dai na kan hanyarsa ne ta zuwa birnin Paris daga kasar Mauritius a daidai lokacin da daya daga cikin fasinjojin jirgin ya ga wani abu mai kama da agogo da aka ajiye akan wani akwati.
Inda nan da nan ya janyo hakalin masu kula da jirgin, wadanda su kuma suka sanar da matuka jirgin, lamarin da ya sa jirgin ya yi saukar gaggawa a birnin Mombasa da ke Kenya, nan take ne kuma aka kwashe dukkani fasinjoji 459 da ke cikinsa tare da masu kula da jirgin su 14.
Jami’an ‘yan sanda a Kenya sun ce an yiwa wasu mutane shida tambayoyi ciki har da mutumin da ya fara ganin na’urar.
Tuni dai rahotanni suka ce an cire nau’rar kuma babu wani abu da ya yi kama da abun fashewa.