Wani Jigon APC A Gombe Ya Koma PDP, Ya Caccaki Gwamnati Kan Almundahana Wajen Ciyar Da Dalibai

APC, PDP

Barde yace akan ware naira miliyan 49 ga makarantun sakandare 42 a jihar, da ke da yawan dalibai 16,411 a kasafin kudin jihar a duk shekara, inda ya bayyana hakan a matsayin wata kulalliya ta yin almundahana.

Wani babban jigo kuma tsohon dan kakarar gwamnan jihar Gombe a karkashin inuwar jam’iyyar APC Muhammad Barde ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Muhammad Barde ya sanar da hakan ne a wajen wani taro da aka yi a jihar ta Gombe, inda kuma ya ja kunnen gwamnatin kan rashin ciyar da daliban makarantun gwamnati a jihar.

Barde yace akan ware naira miliyan 49 ga makarantun sakandare 42 a jihar, da ke da yawan dalibai 16,411 a kasafin kudin jihar a duk shekara, inda ya bayyana hakan a matsayin wata kulalliya ta yin almundahana.

Karin bayani akan: APC, PDP, jihar Gombe, Nigeria, da Najeriya.

Ya ce gwamnatin jihar tana amfani ne da naira miliyan 49.9 wajen ciyar da daliban a shekara guda, wanda hakan ke nufin tana kashe naira 8 a wuni, ko naira 2 da kwabo 70 ne kacal don ciyar da kowane dalibi sau uku a rana.

Da yake jawabi a wurin taron,shugaban jam’iyyar PDP a jihar Manjo janar Abnor Kwaskebe mai ritaya, yace wasu na kan hanyar komawa jam’iyyar PDP a jihar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin ita kan ta jam'iyyar ta PDP mai adawa take rasa manyan jiga-jiganta, ciki har da gwamnoni, da suke sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a sassan kasar daban-daban.