Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi kashedi ga gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle, akan kudurinsa na sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wani taron gaggawa na shugancin jam’iyyar, sakataren watsa labarai na jam’iyyar Kola Ologbondiyan, ya ce PDP za ta kalubalanci matakin gwamnan a kotu, muddin ya koma jam’iyyar ta APC.
PDP na ganin wajibi ne gwamnan ya sauka daga mukaminsa da zara ya sauya sheka daga jam’iyyar, “domin ba wata doka da ta ba shi damar sauya sheka tare da kujerar gwamna da kotu ta baiwa babbar jam’iyyar adawa” a jihar.
Ologbondiyan ya bayyana cewa hakan ba zai yiwu ba domin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, bai bayar da dama ga ‘yan takara masu zaman kan su ba.
Jam’iyyar ta PDP dai tana dogaro ne da sashe na 221 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999, kamar yadda kotun koli ta ambata a shari’ar Faleke da hukumar zabe ta INEC a shekarar 2016.
Karin bayani akan: APC, PDP, gwamnan, jihar Zamfara, Kola Ologbondiyan, Bello Matawalle, Abdullahi Umar Ganduje, Nigeria, da Najeriya.
“Wannan ya nuna karara cewa jam’iyyar siyasa ce ke tsayawa takarar zabe, jam’iyya ce ake kadawa kuri’a, haka kuma duk wani dan takara da aka sanya takarar zabe yana wakiltar jam’iyyarsa ne,” a ra’ayin PDP.
Haka kuma jam’iyyar ta gargadi dukan ‘yan majalisar dokoki na tarayya da na jihar ta Zamfara, da kada su yarda su sauya sheka, domin hakan na iya sa su rasa mukamansu.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa zababbun ‘yan majalisar dokoki damar sauya sheka tare da mukamansu ne kawai idan aka sami baraka a cikin jam’iyyar da aka zabe su.
To sai dai PDP ta ce “ba wata baraka a jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, da za ta baiwa ‘yan majalisar dokoki damar ficewa daga jam’iyyar da mukamansu.
Yanzu haka kuma jam’iyyar ta PDP ta rusa shugabancin jam’iyyar a jihar ta Zamfara.
Wasu majiyoyi kuma na bayyana cewa akwai alamun mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara, ba zai shiga sahun sauya shekar ta gwamna ba.
Majiyoyin da ke da kusanci da sakatariyar PDP ta kasa, sun ce mataimakin gwamnan wanda dan tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara ne kan sha’anin tsaro Ali Gusau, ya nuna rashin amincewa da bin gwamna Bello Matawalle zuwa APC.
Haka kuma akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu manyan jami’an gwamnatin jihar ma ba za su bi gwamnan a sauya shekar ba.