Kudin da alhazan suka biya sama da nera miliyan talatin wani jami'in hukumar alhazan jihar Neja ya wawuresu.
Amma bayyanai na nuna cewa shi jami'in hukumar alhazan mai kula da karamar hukumar Bosso Alhaji Bala Barkuta ya shiga hannun hukumomi domin gudanar da bincike a kanshi.
Maniyyatan da abun ya shafa suna cikin fargaba. Alhaji Abubakar daya daga cikin wadanda abun ya shafa yace sun yi bakin ciki da abun da ya faru amma suna neman taimako daga gwamnan jihar ya sa baki domin mafi yawansu da suka biya kudin manoma ne, daga noma sai kasuwanci ta haka suka tara kudaden. Binta wadda tayi shirin tafiya hajjin tace abun ya taba masu hankali.
Tuni hukumar jin dadin alhazan jihar tace ta dauki mataki kamar yadda Alhaji Sani Awal jami'in hulda da jama'a na hukumar ya shaida. Yace sun riga sun kori jami'in da yayi sama da fadi da kudin. Dangane da ko mutane hamsin din da abun ya shafa zasu tafi aikin hajjin, Alhaji Sani Awal yace da yaddar Allah duk zasu tafi.
Ita gwamnatin jihar Neja tace lamarin ya tayar mata da hankali tare da nuna damuwa akan batun. Alhaji Shehu Haruna kwamishanan ma'aikatar kula da harkokin addinai a jihar yace basu ji dadi ba domin jami'in shi ne shugaba na jihar Neja gaba daya akan aikin hajji. Yanzu suna ba mutanen hakuri yayin da aka kafa kwamitin bincike da zai bada rahoto cikin lokaci mai kankanci.
Masu nazarin al'amura na fatan Allah Ya ceto mutanen da abun ya shafa ganin yadda abun ya faru daidai lokacin da aka ji shiru game da makomar wani alkalin kotun shari'a dake Zungeru a jihar wanda ya kwashe shanu sama da dari biyu na wasu Fulani domin biyan diyar laifin da wani danuwansu yayi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5