Jakadan shugaban Amurka na musamman a Ukraine yayi murabus jiya Jumma’a, a cewar kafofin yada labaran Amurka da suka ambaci majiyoyin dake da masaniya akan batun.
Rahotannin sun ce Kurt Volker ya yi murabus daga mukamin sa bayan da ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo jiya Jumma’a. Nan take dai ma’aikatar harkokin wajen Amurka bata ce komai ba bayan da aka tuntube ta game da batun.
An ambaci sunan Volker a korafin wani mai kwarmata bayanan sirri da ya haddasa fara binciken yiwuwar tumbuke shugaba Trump. Bayanan korafin sun nuna cewa Volker ya taimaka wajen shirya wata ganawa da aka yi tsakanin lauyan Trump Rudy Giuliani da jami’an Ukraine.
Mai kwarmaton da ba a bayyana ko wanene ba, ya yi zargin cewa ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata, a lokacin wata hirar wayar tarho, Trump ya nemi taimakon sabon shugaban Ukraine akan ya nemo wasu bayanan da zasu alakanta tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden da dansa Hunter da wani laifi don gurgunta neman takarar Biden a karkashin jam’iyyar Democrat a zaben shekarar 2020 dake tafe.