Dan Najeriya, dan asalin jihar Lagos, Bayode Preciuous Olawumi ya shafe sa'o'i 120 ko kwanaki biyar yana karatu har ya karance littafai 17 a wata gasa da aka gudanar a birnin Lagos.
Da wannan nasarar Bayode Olawumi ya zama sabon gwarzon sarkin karatu ko alkudukudu na duniya. Wannan bajintar Bayode Olawumi mai 'ya'ya uku ya yi ya doke wanda yake rike da kambu a can baya, wato wani dan kasar Nepal mai suna Diparo Sharmak wanda ya yi nashi karatun na har tsawon sa'o'i 113 da mintuna 15.
Ta bakin Bayode Olawumi karatun ba abun wasa ba ne, bashi da sauki duk da cewa bayan kowane awa daya akwai hutun minti biyar Injishi hutun ba wani abu ba ne domin akwai wani lokaci da ya yi zaton zai mutu ne. Ina shesheka sama sama, a cewarsa.
Tuni dai shi sabon sarkin karatun duniya ya gana da gwamnan Lagos Akinwumi Ambode. Gwamnan ya sha alwashin taimaka masa kana ya nadashi jakada na musamman na karatu da zummar bunkasa harkokin ilimi a jihar da Najeriya baki daya.
Mr. Olawumi ya ce yana murna zai zama abun koyi ga mutane tare da samun karfafawa daga bajintarsa. Ya ce "Kasashen turai da suka ci gaba ba da raye raye ko annashuwa ko nishadi suka ci gaba ba. Da ililmi suka dogara. Karatu da yin nazari da bincike bincike suka ci gaba.
Gasar, gwamnantin jihar Lagos da wasu kamfanoni masu zaman kansu suka dauki nauyin shiryata a kokarin da gwamnatin ke yi na cusawa 'yan jihar dabi'ar karance karance domin samun ilimi.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5