Dama ana takaddama kan sa iya harshen Yarbanci a matsayin daya daga cikin sharuddan shiga makarantun gaba da sakandare a jahar Ikko, sai kuma gashi an kara daukaka al’amarin ta yadda a yanzu a kowace safiya sai ‘yan makarantan sun raira taken Najeriya da harshen Yarbanci, al’amarin da wasu da ba Yarbawa ba ke fassarawa da wani yinkuri na tilasta masu koyo da kuma amfani da harshen Yarbanci.
Daya daga cikin masu nuna damuwa kan wannan al’amarin shi ne Alhaji Ado Dansudu, wanda ke da ‘ya’ya a Makarantun birnin Ikko. To amma y ace muddun ba za a maida abin ya zama kabilanci ko wata hanyar wariya ba, babu wata matsala saboda, a ta bakinsa, “kowane tsuntsu kukan gidansu ya ke yi.” Ya ce a jahohin arewacin Najeriya ma akwai wasu matakai shigen na Ikkon.
Shi kuwa wani tsohon malami mai suna Muhammad Sani ya ce ya kamata a daidai lokacin da ‘yan siyasa su ke la’akari da ribar da za su samu a siyasance kan duk wani mataki, su kuma yi la’akari da tasirin abin kan daukacin jama’a da kuma kasa baki daya.
Ga wakilinmu na Ikko Babangida Jibrin da cikakken rahoton:
Facebook Forum