Wani Dan Bingida Matashi Ya Kashe 'Yan Makaranta 18 A Jihar Texas

Wasu daga cikin iyaye da 'yan uwan yaran da aka kashe a Uvalde da ke jihar Texas a Amurka, Mayu 24, 2022.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce tilas ne a dauki matakin kawo karshen asarar rayuka da ya zama ruwan dare a kasar sakamakon hare haren kan mai uwa da wabi da 'yan bindiga ke yi.

. Shugaba Joe Biden da yake cike da damuwa da bakin ciki, ya yi kira da a yi sabbin dokokin bindiga a daren jiya Talata bayan da dan bindiga ya kashe yara 18 a wata makarantar firamare ta Texas.

"Dole ne mu dauki mataki," Biden ya fadawa al'ummar kasar, bayan shekaru da suka gaza zartar da sabbin dokoki.

shugaba Joe Biden yana jawabi kan kisan kan mai uwa da wabi na jihar Texas

Shima shugaban ilimin makarantun firmare a jihar Texas inda wani matashi mai shekara 18 ya harbe ya kashe yara 18 da manya uku, ya ce lamarin babban abin tashin hankali ne.

Hal Harrell, mai kula da makarantu a gundumar Uvalde, ya fada jiya Talata cewa, za a rufe makarantar firamare ta Robb kuma za a soke duk wasu ayyukan makaranta har sai an sanar da mataki na gaba. Harrell ya kuma ce za a samu masu ba da nasiha kan tashin hankali daga safiyar Laraba.

Adadin wadanda suka mutu ya karu da yammacin jiya Talata. Sanata Roland Gutierrez na jihar ya ce 'yan sandan jihar sun sanar da shi sabbin mace-macen da aka samu daga makarantar ta Uvalde, inda al'ummar Latino suka fi yawa mai tazarar mil 85 yamma da San Antonio.

Wadansu iyayen yaran makarantar firamare ta Uvalde, Texas, May 24, 2022.

Baya ga mutuwar mutane 21, mutane uku da suka jikkata sakamakon harbin sun samu munanan rauni, kamar yadda Gutierrez ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press. Dan bindigar ya mutu, mai yiwuwa 'yan sanda ne suka kashe shi.

Motar daukar marasa lafiya ta kwashe yara 13 zuwa asibitin Uvalde bayan da aka samu rahoton wani mai Harbin kan mai-uwa-da-wabi a makarantar firamare ta Robb da ke Uvalde, kimanin kilomita 135 yamma da San Antonio, in ji jami’an asibitin. Ba a dai san yanayi da munin raunukan da mutanen suka samu ba, kamar yadda ba a san ko an hada da wadanda suka mutu a cikin wannan adadi ba.

Jami'an tsaro a makarantar da aka kai hari a jihar Texas

Wani asibiti kuma na Jami'ar San Antonio, ya ce wata mata mai shekaru 66 tana cikin mawuyacin hali.