WASHINGTON, DC —
Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, ta kama wani Boka, da yayi lalata da ‘yayan cikin sa mata su biyu da ‘yayan kauwarsa suma su biyu ya kuma sa masu cutar HIV.
Bokan mai suna Awoniyi dan kimanin shekaru sittin da biyar zuwa saba’in, yana yin sindabaru da wani bakin sabulu ne wanda yake basu suyi wanka da shi kafi ya fara lalata dasu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Oyo, Muhammad Musa Katsina, yace za’a cigaba da bincike daga bisani a gurfanar da shi a gaban kuliya. Ya kuma sha alwashin ganin cewa zasu cigaba da neman irin wadannan bata gari duk inda suke a cikin al'uma.
‘Yayan nasa dai shekarun su goma sha hudu da sha biyar ne.