Wani Bincike Ya Nuna 'Yan Gudun Hijira 2000 Ke Neman Tallafi A Bauchi

Bincike na nuni da cewar kimanin 'yan gudun hijira dubu biyu ke samun mafaka a sassa dabam dabam a jihar Bauchi, da suke neman tallafi ta fuskar muhalli, da abinci, da kuma samun sana’ar yi domin dogaro da kai.

Kamar yadda binciken ya nuna, 'yan gudun hijiran suna zaune ne a manyan garuruwan jihar da suka hada da fadar jihar, da kewaye, da garuruwan Azare, da kuma Misau, inda suke zaune a gidajen jama’a, da kuma gidajen haya.

Shugaban 'yan gudun hijiran mazauna jihar Bauchi Malam Buba Musa Shehu, yayi jawabi a taron da suka gudanar domin yin nazarin halin da 'yan gudun hijiran ke fuskanta.

A halin da ake ciki kuma, wakilan kwamitin farfado da shiyyar Areaw Maso Gabas sun kai ziyara jihar Bauchi domin ganewa idanunsu halin da 'yan gudun hijiran ke ciki. Shugaban kwamitin Manjo Janar Paul Tarfa mai ritaya ya tabbatar wa 'yan gudun hijiran samin tallafin kwamitin, dangane da koke koken dasuka gabatar.

Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Abubakar Ahmed Kari wanda shine ya jagoranci tawagar kwamitin farfado da shiyyar Arewa Maso Gabas zuwa wurinda 'yan gudun hijiran suka taru, yayi bayani a hukumance tare da ganawa da 'yan gudun hijiran.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Bincike Ya Nuna 'Yan Gudun Hijira 2000 Ke Neman Tallafi A Bauchi