Wani Babban Jirgin Yakin Najeriya Ya Bata A Filin Daga

Jirgin yakin Najeriya mai daukar sojoji da manyan makamai.

Hedkwatar rundunar mayakan daman Najeriya tace wani jirgin yakinta Samfurin Alpha Jet ya bace a jihar Borno.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar sa safiyar yau, yace jirgin ya tashi ne daga sansanin mayakan saman a birnin Maiduguri don marawa dakarun kasa dake fafatawa da 'yan ta'addan Boko Haram.

Kwamandan ya bayyana cewa, an daina jin duriyar jirgin jim kadan bayan tashinsa, kuma yanzu haka ba a san halin da jirgin yake ciki ba.

Sai dai rundunar mayakan saman ba ta bayyana adadin jami'an sojojin da ake cikin jirgin ba a lokacin da ya bace, ko kuma ainin inda ya nufa.

Karin bayani akan: Boko Haram, Maiduguri, Nigeria, da Najeriya.

Rundunar mayakan saman dai tuni ta kaddamar da binciken gano ainihin abin da ya faru da jirgin yakin, kuma tace za ta yi wa jama'a cikakken bayani da zarar an bincike ko kuma an tantance masababin bacewar jirgin.

A watan Fabrairu mayakan sama bakwai su ka mutu a wani hadarin jirgi da ya auku a babban jim kadan bayan tashin shi daga tashar jirgin sama da ke Abuja.

abin-da-shugaba-buhari-ya-fadawa-majalisar-tsaron-najeriya

mun-tattauna-da-buhari-akan-matsalar-tsaro---kayode

buhari-na-jajen-mutuwar-mace-ta-farko-da-ta-fara-tuka-helikwaftan-yaki-a-najeriya