An fitar da sunayen ‘yan wasa uku Lionel Messi da Neymar da kuma Cristiano Ronaldo, wanda daga cikin sune za’a fitar ‘dan wasan da zai zamanto zakaran Ballon d’Or na wannan shekara ta 2015.
Messi ne ake kyautata zaton zai sami kyutar, bayan da ya jagoranci kungiyar Barcelona lashe kofi har uku a kakar wasan da ta gabata. Idan har aka ambace shi a matsayin wanda ya cinye to wannan zai zamanto karo na hudu kenan da ya samin wannan lambar yabon.
Yanzu haka dai Cristiano Ronaldo shine ke rike da kyautar ta shekarar da ta gabata, Ronaldo dai zai yi fatan samun nasarar Ballon d’Or ta wannan shekarar wanda hakan na nufin zai kamo takwaransa Messi a yawan samun kyautar.
Shi kuma Neymar wannan karon zai zamanto kusa da abokin wasansa Messi a bukin mika kyautar, a kakar wasan da ta wuce ne Neymar ya shiga layin zaratan ‘yan wasan da suka fi kowa jefa kwallo raga a wasan La Liga, inda da kwallaye 22 ya shiga gaban Messi da Suarez.
Za dai ayi bukin bayar da kyautar Ballon d’Or 11 ga watan Janairun shekara ta 2016.