Wane Irin Tasiri Halaand Zai Yi A Manchester City?

Erling Halaand, dan wasan Dortmun da Man City ta sayo

Ana kallon Haaland wanda dan asalin kasar Norway da Kylian Mbappe na kungiyar PSG, a matsayin matasan ‘yan wasan da za su maye gurbin Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a fagen wasan kwallon kafa.

Kungiyar Manchester City ta Ingila, ta ce a ranar 1 ga watan Yuli Erling Haaland zai koma kungiyar.

A ranar Talata City ta bayyana cewa ta yi cefanen dan wasan daga Borussia Dortmund.

Ko da yake, ba a fitar da cikakken bayani kan kwantiragin sayensa ba, amma bayanai sun nuna cewa Dortmund ta mai kudi akan dala miliyan 79, kamar yadda AP ya ruwaito.

Ana kallon Haaland wanda dan asalin kasar Norway da Kylian Mbappe na kungiyar PSG, a matsayin matasan ‘yan wasan da za su maye gurbin Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a fagen wasan kwallon kafa.

Dan shekaru 21, Halaand, wanda dogo ne kakkarfa, ya zura kwallo 85 a wasa 88 da ya bugawa Dortmund tun bayan da ya je kungiyar daga Salzburg ta kasar Australia a watan Janairun 2020.

A baya an sha alakanta shi da kokarin komawa kungiyar Real Madrid ta kasar Sifaniya.

Masu sharhi a fagen kwallon kafa na ganin zuwan Halaand City, zai iya daga darajar kungiyar daga matsayinta na mai lashe kofin gasar Premier zuwa fitacciyar kungiya a nahiyar turai.

Kungiyar ta City, wacce ke karkashin jagorancin Pep Guardiola, ta gaza lashe kofin gasar Champions League, duk da kyakkyawan cefanen zaratan ‘yan wasan da ta yi.