Kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari a Najeriya na nuna damuwa kan yadda walwalar rayuwar Jama’a da martaba muradun su ke samun koma baya a kasar.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ta shafe fiye da shekaru 20 akan tafarkin dimokradiyya, wanda salon mulki ne dake ba da kariya ga muradun ‘yan kasa.
Majalisun dokoki, kafofin labarai da ke aiki bisa kwarewa da ‘yanci, kungiyoyin fararen hula, tsarin shari’a na adalci, na daga cikin ginshinkan wanzar da shugabanci na gari a fasalin da salon mulki irin na dimokradiyya wadda ke martaba ra’ayi da muradun ‘yan kasa ta kowace fuska.
A cewar Comrade Abdulrazak Alkali Daraktan kungiyar OCCEAN a Kano, wadannan muradu na daga al’amuran da kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari ke yi wa lakabi da Civic Space da turanci, kuma suke kokarin ganin an cimma a Najeriya.
“Duk lokacin da aka ce civic space muna nufin wani yanayi da yake bayar wa ga al’umma ‘yan kasa, kungiyoyi, ‘yan jarida su samu kafa ta walwala, mu’amala ta bibiyar yadda gwamnati take gudanar da abubuwanta na maganar samun bayanai, na maganar tuntuba, don su ji yaya abu yake gudana da bukatar son a zauna da su a tattauna domin inganta al’umma a cikin tsarin dimokradiyya.”
Ko da yake, an samu nasarori a Najeriya bayan da kasar ta koma tafarkin dimokradiyya kusan shekaru 20 da suka gabata, amma samar da yanayin da ke tabbatar da walwala da sauran muradu ga ‘yan kasa ya samu koma baya a baya bayan nan.
“Domin gwamnatoci kamar sun fara fito da wasu tsare-tsare na dokoki da suke kokari su takure wannan ‘Yanci na al’umma wanda kuma shi ne ba ma jin dadi, kuma mutanen da suka so su yi zanga-zanga domin bayyana ra’ayinsu kan abubuwa da ba su jin dadi a wannan yanayi da ake ciki." In ji Comrade Alkali.
Sai dai Sanata Mas’ud El Jibril Doguwa da ya yi shugaban karamar hukuma a zamanin mulkin soja, kuma tsohon wakili a majalisar dattawan Najeriya ya fayyace dalilan koma bayan.
“Abin da ya sa aka samu koma baya, ba wani abu ba ne son zuciya ne, daga kan shi wadda ake mulka da kuma wanda yake mulki. Shi wanda yake mulki dama ba ya so ya je ya fada maka me ka ke so, shi kuma wanda ake mulka, idan ya zo wajen ka kawai ya tunanin abin da zai saka a aljihunsa, amma a da kungiyoyi na aikin gayya, na sa kai, na hada kai a unguwanni da garuruwa suna taka rawa muhimmiya a wajen wannan al’amari saboda sune suke tare da mutane." In ji Sanata Doguwa.
Tuni dai masana kimiyyar siyasa suka yi tafsirin dimokradiyya a matsayin gwamnatin da aka kafa domin biyan muradun Jama’a.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5