Wakokin Jan Hankalin Matasa Kan Muguwar Dabi'a - Mahdi Danko

Mahdi Danko

Na kan yi wakokin fadakarwa kuma mussaman na fi maida hankali a bangaren dabi’ar rayuwar samari da ‘yan mata dangane da yadda rayuwa ta canza, kwadayi ya fi yawa a harkar soyayyar matasa inji matashin mawaki Mahdi Danko.

Mahdi Danko, ya bayyana cewa a wata wakarsa da yayiwa lakabi da “A bi sannu” ya ja hankalin matasa akan yadda wasu samari ke amfani da matsala ta talauci ko ta kwadayin abin duniya su lalata ‘yan mata da wasu dabi’u marasa kyau da ba na malam Bahaushe ba.

Ya ce matsalar matsin rayuwa ya haddasa wasu iyayen basa iya kula da iyalinsu yadda ya kamata, kuma mafi yawan lokutan ‘yan mata sai suyi amfani da rashin da iyayensu ke fama da shi su rika bin samari domin samun kudin kashewa ba tare da iyaye sun yi li’akari da daga ina ‘ya’yan su suka samo kudi.

Ku Duba Wannan Ma Yaki Da Kalaman Batanci Ya Sa Na Fito Da Sabuwar Waka - Double Haske

Ya kara da cewa a yanzu a cikin kimanin matasa kaso 10, cikin dari, samari uku ne kadai zasu iya kamewa ba tare da sun saba hanya ba wajen cutar da ‘yan matan su da wasu dabi’u wala Allah na kudi da aikata alfasha ko shigar da su hanyoyin shaye shaye.

Sabanin sauran mawakan da suke yankin Kanon Dabo a wannan karo Mahdi Danko, yayin zantawar sa da wakiliyar dandalinvoa, manajansa mai suna Hamza Hassan Inuwa wanda aka fi sani da Hamza planner, ya ce sun dauki wannan tsari ne domin dauke masa matsalolin da zai iya fuskanta daga bangaren al’umma gudun kada hakan ta shafi harkarsa ta waka.

Your browser doesn’t support HTML5

Wakokin Jan Hankalin Matasa Kan Muguwar Dabi'a - Mahdi Danko 7' "29"